Labarai

Yadda EFCC ta kama Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, bisa almundahana da karkatar da kudade da yawansu ya kai Naira miliyan dubu 80

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a jiya sun kama Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, bisa zargin almundahana da karkatar da kudade da yawansu ya kai Naira miliyan dubu 80.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, hukumar ta tabbatar da bayanan sirrin da ta samu dake bayyana cewa Akanta Janar na tarayya ya wawure kudaden ne ta hanyar kwangiloli na bogi da sauran ayyukan da suka sabawa doka ta hanyar amfani da ‘yan uwa, iyalai da makusanta.

An yi almundahanar kudaden ne ta hanyar zuba jari a Kano da Abuja.

An kama Ahmed Idris ne bayan ya ki amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa domin zuwa ya amsa wasu tambayoyi da suka shafi cin amanar kasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: