Cif Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya bayyana cewa wasu fitinannun gara da zago ne suka cinye masa takardar shaidar kammala karatun firamare din sa.
Muhammad ya ce gara da zago sun shiga dakin da ya ke ajiye shirgin takardun sa, a gidan sa na Bauchi a cikin 1998, inda suka durfafi dukkan takardun sa, sai da suka cinye su karkaf.
Ya ce cikin kayan sa da aka cinye har da satifikef din sa na kammala firamare.
“Sun cinye komai, ba su bar ko da wata guntuwar takarda ba.”
Haka ya rubuta a cikin wata rantsuwar-kaffarar-kwansitushin da ya aika wa Majalisar Dattawa domin neman amincewa a nadin da Buhari ya yi masa.
Tanko ya yi ‘rantsuwar kaffara’ a ranar 13 Ga Fabrairu, 2002, a lokacin ya na mai shari’a a Kotun Daukaka Kara ta Jos, Jihar Filato. Ya zama Mai Shari’a a Kotun Koli cikin 2007.
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Cif Jojin Tarayya, bayan ya cire Cif Joji Walter Onnoghen daf da zaben 2019.
Jim kadan bayan nada shi, sai sai wani lauya ya shigar da karar zargin sa da kantara karyar rage yawan shekaru haihuwar sa.
An yi zargin cewa ya rage shekara uku, daga 31 Ga Disamba, 1950, zuwa 31 Ga Disamba, 1953.
Muhammad Tanko dai ya karyata wannan zargi. Shi kuma lauyan da ya maka shi kotu, aka kori karyar tare da cin shi tarar naira milyan 10.
Mai Shari’a ya ce lauyan ba shi da ikon shigar da waccan kara, kuma ba ta ma da wani tushe ballantana hurumi.