Babbar Jam’iyar Adawa ta PDP ta lashe zaben kujerar Kamsilan Mazabar Chiyako na karamar hukumar Birnin Kudu a nan Jihar Jigawa.

Kafin zaben da aka gudanar a ranar Asabar Jam’iyar APC ce take mulkar Birnin Kudu, wanda kuma nan ne karamar hukumar tsohon gwamna Sule Lamido.

Jami’in Tattara Sakamakon Zabe na Mazabar Malam Balarabe Umar ya bayyana cewa Yunusa Abdul na Jam’iyar PDP ya samu kuri’u dubu 3,952, inda kuma Yusuf Umar na APC ya samu kuri’a 680.

Sai dai Jam’iyar APC ce ta lashe zaben Kamsiloli da shugabannin kananan hukumomi da aka gudanar a fadin jihar nan.

Tun da farko Masu zaben sun killace Ma’aikatan zaben na Mazabar Chiyako a wani mataki na dakile magudin zabe.

Kimanin Ma’aikatan Zabe 30 aka killace a mazabar, ciki harda yar gidan Mataimakin shugaban Karamar hukumar Birnin Kudu na yanzu Ramla Isah saboda kin bayyana sakamakon zaben.

Amma daga baya, an sanar da sakamakon zaben a Makarantar Firamaren Chiyako wanda ita ce Cibiyar tattara sakamakon Zabe a mazabar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: