Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Femi Gbajabiamila, yace dole a sanya ido akan kafafen sada zumunta na zamani domin hana kasarnan fadawa cikin matsala.

Yace majalisar kasar ta jima tana yunkurin iyakance amfani da kafafen sada zumunta na tsawon lokaci, amma tana Dari-Darin aiwatar da hakan saboda ‘yan Najeriya sun bayyana rashin amincewarsu.

Kakakin Majalisar wanda ya amince da alkhairan na shafukan saba zumunta yake dasu, ya kuma yi nuni da cewa kafafen sada zumunta ne manyan makamai wanzar da alkhairi da kuma sharri.

Gbajabiamila ya sanar da haka a jiya ta wani shirin gidan talabijin na Channels.

Sai dai, matsayar ta Gbajabiamila ta dora alamar tambaya akan binciken da majalisar wakilai ke yi dangane da haramta Twitter.

A ranar 4 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da Twitter a Najeriya.

Wannan Matakin na gwamnati yazo kwanaki kalilan bayan shafin na twitter ta goge wani bayanin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: