Kotu ta yanke hukuncin daurin sama da shekara 20 ga wanda ya kashe bakar fata a Amurka

0 96

Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 22 da rabi kan tsohon dan sandan Amurka Drek Chauvin da aka samu da laifin kashe George Floyd bakar fata a birnin Minneapolis.

Yayin zartas da hukuncin, Alkali Peter Cahill ya ce babu alaka tsakanin matsayar kotu kan hukuncin daurin da batun tausayi, ko ra’ayin mutane.

Tun da farko daurin shekaru 30 masu gabatar kara suka nemi a zartas kan tsohon dan sanda saboda kashe George Floyd da yayi.

A karkashin doka dai Chauvin ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 30 kan tuhumar kisan gillar da aka yi masa, sai dai dokokin jihar Minnesota inda yake aiki sun ce kamata yayi tsohon dan sandan ya fuskanci hukuncin shekaru 12 da rabi, la’akari da cewar hukuma ba ta taba samunsa da aikata wani laifi ba.

Cikin watan Mayun shekarar 2020 kisan George Flyd ya janyo barkewar zanga-zanga a wasu biranen Amurka da suka hada da New York, Washington, Atlanta, Los Angeles da Minneapolis dake jihar Minnesota, inda boren ya samo asali.

Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda dan sanda ya taka wuyan bakar fatar da gwiwarsa tsawon mintuna, wanda daga bisani ya mutu sakamakon rashin shakar iska duk da cewar Floyd ya nemi ya bashi damar numfasawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: