Gwamnan Bello Matawalle ya fitar da miliyan 100 ga masu rubuta WAEC

0 124

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya amince da fitar da Naira Milyan 100 ga hukumar kula da Jarabawar Africa ta yamma WAEC a matsayin kudin jarabawar daliban da zasu rubuta jarabawar WAEC a jihar 2021.

Da yake biyan kudin a jiya juma’a Gwamnan ya nuna godiyar sa ga Ministan ilimi kan WAEC kan fahimtar da sukayi da kuma kula da harkar ilim a jihar duk da bashin da hukumar jarabar WAEC ke bin jihar a matsayin abin da ta gada daga gwamnatin da ta gabata.

Gwamna Matawalle yace ma’aikatar ta tallafawa jihar ta hanyar bada dukkan abubuwan da ake bukata ga daliban da zasu zana jarabawar ta WAEC ciki harda sakin sakamakon su, da basu damar rubuta jarabawar da zata biyo baya.

Yace gwamnatin sa zata ci gaba da sauke nauyin dake kanta amatsayin wani bangare na matakin da ta daukawa al’umma musamman matasa masu tasowa ta hanyar samar da ingantaccen ilimi a jihar.

Gwamnan ya sake jadda cewa kasancewar ilimi shine hanyar samun daukaka, don haka bangaren ilimi zai samu babban fifiko a karkashin Gwamnatinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: