Yadda ‘yan bindiga suka sace mataimakin shugaban karamar hukuma a Jihar Kaduna

0 104

Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban karamar hukumar Jaba na Jihar Kaduna, Mr James Bijimi tare da wani da ba’a bayyana a hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Lamarin ya faru ne Bayan yanbindigar sun kashe wani direba tare yin garkuwa da wasu mutane 33 a cikin garin na Kachia.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce jami’an tsaro sun kwato motoci guda 3 wadan ake kyautata zaton na wadanda aka sace ne, ya yin da mutun guda ya samu rauni.

Wani shugaban yankin da aba’a bayyan sunansa ba ya fawa manema labarai cewa yan fashin sun kewaye gonar Roger da Makyali a karamar hukumar Kajuru da karfe 10 na safiyar jiya.

Jami’an sun maida martani ga yan bindigar inda suka fafata dasu, kuma suka samu nasarar cetan matan da aka sace.

Wani babban jami’in karamar hukumar ya shidawa gidan Television na Channels cewa yan bidigar suna neman kudin fansar mataimakin shugaban karamar hukumar Jaba Naira Milyan 100.

Leave a Reply

%d bloggers like this: