Sheik Ahmad Gumi ya karyata rahotannin da ke cewa DSS ta gayyace shi

0 87

Malamin addini Islama Sheak Ahmad Gumi ya karyata rahotannin da ke cewa hukumar tsaro ta DSS ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kan kalaman da yayiwa sojoji.

Da yake magana da gidan Television na Channels bayan jagoranci sallah juma’a a masallacin Sultan Sokoto dake jihar Kaduna a jiya juma’a.

Sheak Gumi ya ce duk ayyukan da yake yi da yamfashin daji yanayin sune da hadin gwiwar gwamnati tare da hukumomin tsaro don haka baiyi wani laifi ba.

Gumi ya kuma dage kancewa baitabayin wasu kalaman batanci ga sojoji ba, a cewar sa babu wasu kalaman suka da yayi ahirarsa da gidan Television na Channels.

A ranar juma’ar da tagabata ne hukumar tsaro DSS tace ta gayyaci Sheak Gumi don amsa tambayoyi.

Hukumar ta DSS bata tabbatar da dalilin wannan gayyatar ba, amma hakan bazai rasa nasaba da yadda Gumi yake fito na fito da batun yan fashi a Nigeria ba.

Malamin yayi Imani cewa ya kamata ayiwa yan fashin afuwa wanda yace an tilastasu zuwa aikata laifuka sabo da wani bangare na rashin kulawar gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: