Yadda mutane 24 suka mutu bayan sunci abinci mai guba a Sakkwato

0 114

Ma’aikatar Lafiyar Jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutane 24 bayan sun ci abinci mai guba, a kyauyen Danzanke dake Mazabar Bargaja a karamar hukumar Isa ta Jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar Dr Ali Inname, wanda ya tabbatar da labarin a cikin wata sanarwa, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Danzanke da ke ƙaramar hukumar Isa.

Ya ce mutanen sun ci abincin ne da aka yi kuskuren amfani da gishirin lalle a madadin gishirin abinci.

Kwamishinan ya ce yanzu haka ana kula da lafiyarsu a asibiti tare  da fatan za su rayu.

Haka kuma ya ce an yi ƙoƙarin ceton ran waɗanda suka ci abincin mai gishirin ƙunshi amma Allah bai nufa ba.

Dr Ali ya ce yana da matukar mahimmanci ga jama’a su san cewa lamarin da ya faru ana iya magance shi domin ba al’amari ba ne da ke yaɗuwa,

saboda yana da matuƙar hatsarin yin kisa, koda kuwa an ba da kyakkyawar kulawar asibiti ga waɗanda abin ya shafa.

Dr Inname ya ce ya kamata wannan ya zama darasi ga al’umma wanda sau biyu kenan hakan na faruwa a bana bayan al’amarin da ya faru a jihar Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: