Daliban Makaranta dubu 600,000 ne zasu shiga cikin tsarin gwamnatin tarayya na ciyar da Yara yan Makaranta a jihar Jigawa

0 145

A kalla Daliban Makaranta dubu 600,000 ne zasu shiga cikin tsarin gwamnatin tarayya na ciyar da Yara yan Makaranta a jihar Jigawa.

Ministar Ma’aikatar Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana hakan a lokacin da take kaddamar da aikin tattara bayanan daliban da za’a saka cikin shirin a Makarantun Fagoji da Shuwarin.

Ministar wanda Mataimakin Daraktan Ma’aikatar Badayi Mukthar, ya wakilta, ya bayyana cewa an kirkiri shirin ne domin a rika ciyar da daliban makarantun Aji 1 zuwa 3 na Firamare su kimanin dubu 641,295 daga kananan hukumomi 27 da suke jihar Jigawa.

Mista Badayi, ya ce aikin rijistar sabbin daliban zai dauko bayanan daliban Firamare dubu 2,211 a makarantun da suke jihar nan.

Haka kuma ya ce kimanin Mata dubu 5,024 ne aka dauka domin su rika yin aikin girkin abincin a jihar Jigawa.

Kazalika, ya ce an kirkiri shirin ne domin ya kara yawan adadin Yaran da suke zuwa Makaranta, tare da samar da abinyi ga Matan da suke girka abincin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: