Kimanin mutane 80 NAPTIP tayi nasarar kubutarwa daga hannun masu safarar su a jihar Kano

0 145

Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) ta ce kimanin mutane 80 ne tayi nasarar kubutarwa daga hannun masu safarar su a jihar Kano.

Kwamandan Hukumar na shiyar Arewa Maso Yamma Malam Abdullahi Babale, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

Malam Babale, ya ce shekarun mutanen da aka kubutar basu wuce 16 zuwa 35 ba, wanda suka kunshi Mata 59 da Maza 21.

A cewarsa, hukumar yan sandan Kasar Nijar ne ta kamo mutanen bayan Jami’an hukumar dake aiki a bakin Boda sun fadawa Ma’aikatan Sunturi na Kasar Nijar kan tafiyar mutane a ranar 9 ga watan Agusta.

Haka kuma ya ce suna cigaba da gudanar da bincike domin kamo mutanen da ake zargin da safarar.

Kwamandan hukumar ya yabawa Jami’an hukumar Shige da Fice ta Kasa wato Immigration wanda suke aiki a Jihar Katsina, bisa yadda suke aiki da hukumar ta NAPTIP wajen kubutar da mutanen.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa a ranar 28 ga watan Yuli kimanin mutane 13 ne tare da mai safarar su guda 1 aka kama a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa kasashen Nijar da Libya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: