Za a kashe Dala Miliyan 2.5 da Naira Miliyan 498.23 domin bunkasa wutar lantarki a Najeriya

0 72

A wani Labarin kuma Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince Kashe Dala Miliyan 2.5 da kuma Naira Miliyan 498.23 domin aiwatar da wasu ayyuka bunkasa wutar lantarki guda 4 a kasar baki daya.

Cikin ayyukan da za’ayi da kudaden sun hada da Saya tare da sake gyara Na’urorin Taransfoma, da Na’urar Circuit da sauran kayayyakin da wutar lantarki take nema domin sake inganta wutar a kasa baki daya.

Ministan Ma’aikatar wutar Lantarki Engineer Saleh Mamman, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala zaman majalisar zartarwa wanda Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Ministan ya ce ayyukan sun hada da dasa wasu Na’urori a Kamfanin Samar da wutar Lantarki ta Kasa wanda zai ci kudi kimanin Dala Miliyan 502,950 da kuma wasu kudade kimanin Miliyan 15 da dubu 800.

A satin daya gabata ma, Majalisar ta amince sake gina wasu Cibiyoyin Wutar Lantarki a Jihohin Jigawa da Akwa Ibom wanda zasu cinye kudade kimanin Naira Miliyan 454 da kuma wasu Dala Miliyan 6.2

Leave a Reply

%d bloggers like this: