Ana cigaba da Shirin Tallafi na Musamman na karamar hukumar Hadejia ciyar da daliban firamare

0 104

Jami’in Shirin Tallafi na Musamman na Karamar Hukumar Hadejia, Alhaji Musa Ibrahim Baderi ya ce ana gudanar da aikin tantance bayanai na shirin ciyar da dalibai da nufin tsabtace shirin wanda ma’aikatar jin kai ta tarayya ta dauki nauyinsa.

Jami’in shirin ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin tantancewar a makarantar firamare ta Gawuna a nan Hadejia.

Musa Baderi ya ce makarantun firamare 38 da na Tsangaya 9 da ke fadin karamar hukumar an yi musu rajista a matsayin wadanda za su ci gajiyar shirin, inda ya kara da cewa ana sa ran daukar bayanan dalibai dubu 23 da 217.

A jawabinsa na kaddamarwa, Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Hadejia Alhaji Abdulkadir Umar Bala T.O, ya umarci ma’aikatan tantancewar da su yi aiki da gaskiya domin cimma burin da aka sanya a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: