Akalla mutane 146 ne suka mutu a jihar Kebbi dalilin cutar kwalara

0 132

Akalla mutane 146 ne suka mutu a jihar Kebbi, a cewar wani jami’in kiwon lafiya, yayin da cutar kwalara ta bazu zuwa jihar.

An bayar da rahoton yadda barkewar cutar kwalara ke yaduwa a kasarnan inda aka samun yawaitar asarar rayuka a jihoshin arewa maso yamma.

A Jihar Katsina an samu mutuwar 75 ya zuwa jiya, yayin da Zamfara ta ba da rahoton mutuwar mutane 30, Sokoto 23 da Kano 119.

A wata hira ta wayar tarho da safiyar yau, babban sakataren asibitin tunawa da Sir Yahaya a Birnin Kebbi, Aminu Bunza, ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu na jihar.

Ya ce an fara samun labarin bullar cutar a karamar hukumar Sakaba ta jihar.

Aminu Bunza ya ce mutane dubu 2 da 28 ne suka kamu da cutar ya zuwa safiyar yau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: