Dalilan da yasa gwamnatin jihar Borno ta rushe masallaci da coci

0 59

Biyo bayan takaddamar da ta biyo bayan rusa wasu guraren ibada a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta ce binciken da ta yi ya nuna cewa hakika gwamnatin jihar ta rushe masallatai da coci-coci.

Jaridu sun ruwaito cewa an samu cece-kuce a jihar saboda rushe-rushen.

Haka kuma tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, shi ma ya shiga sahun masu adawa da rushe-rushen, inda ya zargi gwamnatin jihar da kai wa coci-coci hari a yayin da ta ke rusa gidaje.

Amma kungiyar kare hakkin Musulman ta bayyana cewa hakika Gwamnatin jihar Borno ta rushe masallatai 11 da coci-coci guda hudu.

Wannan, a cewarta, ya saba da zargin cewa coci-coci ne kadai aka rushe a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: