An samu sabbin mutane 610 da suka harbu da corona a Najeriya, adadi na biyu mafi yawa cikin watanni 6

0 65

A jiya an samu sabbin mutane 610 da suka harbu da corona a Najeriya, adadi na biyu mafi yawa cikin watanni 6.

A wani bayani da ta wallafa a shafin Facebook jiya da dare, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta kara da cewa an kuma samu mutuwar mutane biyu sanadiyyar cutar cikin awanni 24 da suka gabata.

Hukumar tace sabon adadin wadanda suka kamu ya kara yawan wadanda cutar ta harba a kasarnan zuwa dubu 179 da 118, kuma wadanda suka mutu zuwa yau sun kai dubu 2 da 194.

A cewar hukumar ta NCDC, an samu wadanda suka kamu a jiyan a jihoshi 12 da babban birnin tarayya.

Karuwar yawan mutanen dake harbuwa wanda nauin Delta na kwayar cutar ya haifar, yana kuma jawo karuwar wadanda ke mutuwa.

Sama da mutane 30 ne suka mutu sanadiyyar cutar a makon da ya gabata a fadin kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: