Yadda rashin wutar lantarki ta jawo ta barbarewar harkar lafiya a Najeriya

0 79

A asibitin gawmnati daya, jariri ya mutu a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa

Matsalar wutar lantarki a asibitoci a Najeriya ta jefa marasa lafiya cikin halin ni-’yasu, lamarin da ke kara ta’azzara halin da majinyata ke ciki, har ta kai ga asarar rayuwa.

Rashin wuta ya yi sanadin mutuwar jariri a cikin wata mai juna biyu, wata ta yi awa 15 tana jiran a yi mata tiyatan haihuwa, wata kuma ta mutu sakamakon dauke wuta a yayin da ake tsada da yi wa mata tiyata, a Asibitin Jummai Babangida Aliyu, da ke jihar Neja.

’Yan uwa sun shaida wa wakilinmu cewa an shafe sama da kwana uku a jere babu wutar lantarki a asibitin gwamnatin, a yayin da rashin wuta da yanayi na tsananin zafi ya tilasta wa ’yan uwan majinyata amfani da fankoki masu amfani da caji domin samun iska a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Jihar kano.about:blank

Bincikine wakilanmu ya gano matsalar lantarkin na kawo tsaiko ga gudanar a tiyata da ayyukan karbar haihuwa da awon masu juna biyu a asibitoci.

Majinyata a asibitocin da muka ziyarta sun bayyana cewa rashin wutar ta sa ana dage lokacin da aka shirya yi musu tiyata baya ga kawo tsaiko ga sauran nau’ikan aikin kula da lafiya.

Wannan matsala ta shafi asibitocin koyarwa, inda yawan kudin wutar da ake kamfananonin rarraba lantarki ke bin su  ya yi yi musu katutu. Shugabannin asibitocin koyarwar sun bayyana cewa sun yi kokari biyan bashin, amma duk da haka sai sun kara neman wasu kudaden domin samar wa wata hanyar samun lantarki, saboda matsalar rashin samun wutar gwamnati da ta ki ci ta ki cinyewa.

A cikin wannan hali, a watan Fabrairu Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar da shirin sake kara kudin wutar, bisa hujjar cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin lantarki ba.

Leave a Reply