Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sababbin takardun kuɗin naira da ya sauya wa fasali.

An fitar da takardun kuɗin ne yayin bikin da ke gudana yanzu haka a Fadar Shugaban kasa ta Aso Rock Villa a babban birnin tarayya Abuja.

Takardun kuɗin sun ƙunshi N1,000, da N500, da N200.

Babban Bankin kasa (CBN) ya ce daga ranar 15 ga watan Disamba zai baza kudaden ga al’ummar kasar nan don fara amfani da su.

Kazalika, za a daina amfani da tsofaffin takardun a matsayin kuɗi daga ranar 31 ga watan Janairun 2023.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: