Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari a yau ya fara rabon shanu 400 ga magoya bayansa a kananan hukumomi 14 da mazabu 147 na jihar.

Haka kuma daga cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin na bukukuwan Sallah akwai marasa galihu a cikin al’umma.

Shugaban kungiyar Abdulaziz Yari, Lawal Liman, ya mika wasu daga cikin shanun ga wadanda suka amfana yau a Gusau.

Ya lissafa wadanda suka ci gajiyar tallafin da suka hada da malaman addinin musulunci da kungiyoyin matasa da mata da tsofaffi da kuma shugabannin al’umma a jihar.

Ya yabawa tsohon gwamnan bisa yadda yake nuna damuwarsa ga al’ummar jihar musamman marasa karfi.

Lawan Liman ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su samu lokaci a cikin watan Ramadan domin yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma Najeriya baki daya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: