Yadda warin man fetur ya shake numfashin wani direba kuma yayi sanadiyyar mutuwar sa a Kano

0 144

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani mutum dan shekara 45, direban tanka, mai suna Dahiru Aliyu, a NNPC depot dake Hotoro.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar jiya, daga kakakin hukumar, Saminu Abdullahi.

Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Litinin da safe.

Saminu Abdullahi ya bayyana cewa hukumar kashe gobarar ta samu kiran neman daukin gaggawa daga wani mutum mai suna Shu’aibu Muhammad da misalin karfe 10 da mintuna 59 na safe, kuma ba tare da bata lokaci ba aka tura tawagar masu aikin ceto.

Ya kara da cewa Dahiru Aliyu ya shiga daya daga cikin guraren ajiyar mai domin kwarfe man da ya malala, inda warin man ya shake masa numfashi kuma ya mutu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: