Muhammad Shehu, mai bawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano shawara akan harkokin gwamnati, yayi murabus.

Muhammad Shehu ya kuma sanar da sauya shekarsa daga tsagin jam’iyyar APC da gwamnan ke marawa baya, zuwa tsagin dake biyayya ga Mallam Ibrahim Shekarau.

Bayan wani zaman ganawa tare da magoya bayansa a jiya, Muhammad Shehu ya gayawa manema labarai cewa ya yanke hukuncin komawa bangaren shekarau ne tare da dubban magoya bayansa, saboda rashin shugabanci nagari a bangaren Abdullahi Abbas.

Yace shi da magoya bayansa sun yanke hukuncin komawa tsagin Shekarau da nufin yiwa Barau Jibrin kamfen na takarar Gwamna.

Muhammad Shehu yace tsagin Abdullahi Abbas bai yi masa adalchi ba, da shi da magoya bayansa a yankin karamar hukumar Nasarawa, inda ya fito kuma yake da magoya baya.

Muhammad Shehu shine jami’in gwamnati na farko da ya sanar da sauya shekarsa, bayan hukuncin kotun da ya rushe shugabannin jam’iyyar dake biyayya ga Gwamna Ganduje.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: