Yadda wasu mutane uku suka mutu yayin da wasu 13 suka jikkata a lokacin da wata tankar gas ta kama da wuta a Lagos.

0 138

Mutane uku sun mutu yayin da wasu 13 suka jikkata a lokacin da wata tankar gas ta kama da wuta a Lagos da tsakar daren jiya.

Tankar da kama da wuta a akan titin Mobolaji a kusa da OPIC plaza da hotel din Sheraton a Ikeja.

An rawaito cewa ma’aikatan ceto sun amsa kiran daukin gaggawa mintuna kadan kafin sha biyun dare, daidai lokacin da tankar ke tafiya zuwa Ikeja.

Hukumar agajin gaggawa ta Lagos (LASEMA) a bayanin da ta fitar dangane da lamarin tace konewar tankar ya shafi OPIC Plaza, lamarin da ya haifar da gobarar da ta lalata motoci 12 da ke ajiye a harabar ginin.

Hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta tabbatar da cewa an gano gawarwaki uku a yau da safe.

Tunda farko, hukumar LASEMA a rahotonta na farko tace an ceto mutane 13.

Leave a Reply

%d bloggers like this: