Yadda wasu ‘yan bindiga dauke da makamai su ka sace dalibai 9 na makarantar Islamiyya a jihar Katsina

0 114

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta ce wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun sace dalibai 9 na makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar.

Wasu mazauna Faskari su biyu da suka zanta da manema labarai sun kara da cewa ‘yan bindigan sun kuma yi awon gaba da daya daga cikin malaman makarantar.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Gambo Isa, ya ce yaran suna dawowa daga Islamiyyar yamma lokacin da aka sace su.

Sakkai wani kauye ne mai nisa daga hanyar da ta hada Faskari da Yankara, wanda hakan ya sa ya zama mai fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

Faskari na daya daga cikin kananan hukumomi 10 na gaba-gaba a jihar, da ake yawan yin garkuwa da mutane da satar shanu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: