Mutum 3 ne suka mutu yayin da wasu 50 suka jikkata bayan wani bam ya tashi yayin da yan Shi’a suke tattaki a Pakistan

0 137

Akalla mutane uku sun mutu yayin da wasu 50 suka jikkata bayan wani bam ya tashi a cikin jerin gwanon ‘yan Shi’a yayin da suke tattaki a tsakiyar Pakistan.

An tsaurara tsaro a yau yayin da ‘yan shi’ar marasa rinjaye a kasar, suka yi bikin Ashura.

Hotunan bidiyo na kafofin sada zumunta sun nuna mutanen da aka jikkata suna kwance a kan hanya cikin jini, yayin da jama’a ke taimaka musu.

Wani dan sandan yankin, Kashif Hussain, shi ma ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ga manema labarai.

Hukumomi sun dakatar da ayyukan wayar salula a manyan biranen kasar a matsayin matakin tsaro a lokacin muzaharar ta Ashura. Mazauna a birane dayawa suna fuskantar rashin service.

An kuma toshe titunan da ake bi domin zuwa wajen tattakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: