Yau itace ranar da za a ɗaura auren Yusuf Bubari da Zahra Nasiru Ado Bayero

0 203


Yau Juma’a itace ranar da za a ɗaura auren Yusuf Bubari da Zahra Nasiru Ado Bayero da misalin da ƙarfe ɗaya da rabi na wannan rana.
Kamar yadda kuke gani, an tsaurara matakan tsaro a gidan Sarkin Bichin da kuma masallacin na garin Bichi, inda za a daura auren amarya da angon.
Tuni dai manyan baƙi wadanda suka hada da sarakuna da jami’an gwamnati da sauransu suka fara isowa Bichin tun sassafe domin halartar ɗaurin auren.
Har yanzu dai ba a samu tabbacin zuwan shugaba Muhammadu Buhari wajen taron ɗaurin auren, amma ana sa rai.
Hotuna: BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: