Yan bindiga a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a yanzu sun koma neman dafaffen abinci a matsayin kudin fansar wadanda suka sace.

An bayyana cewa ‘yan bindigan sun rage hare-hare kan kauyuka tun lokacin da gwamnatin jihar ta hana kasuwannin mako-mako a matsayin wani mataki na magance rashin tsaro a jihar.

Wani shugaban matasa a daya daga cikin kauyukan Birnin Gwari, Babangida Yaro, ya fadawa manema labarai cewa tun lokacin da aka hana cin kasuwannin, ‘yan fashi da ke aiki a kauyukan Damari, Kutemashi da Kuyello suka koma neman dafaffen abinci kadai duk lokacin da suka sace mutane.

A cewarsa, hana sayar da mai a gidajen mai da ke yankunan karkara ya taimaka wajen takaita zirga-zirgar su.

Ya kara da cewa duk lokacin da suka yi garkuwa da mutane biyu ko uku a gonaki, ana barin mutum daya ya je ya samo musu abinci daga iyalai a matsayin kudin fansa tunda babu hanyar sadarwar da za a iya tuntubarsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: