‘Yan bindiga dauke da makamai suna ci gaba da kai hare-hare a jihar Zamfara

0 163

An rawaito cewa ‘yan bindiga dauke da makamai suna ci gaba da kai hare-hare kan kauyukan kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi a jihar Zamfara, inda suke kashe mutane da kona gidaje.

Hakan na zuwa ne duk da farmakin da sojoji ke kaiwa kan ‘yan bindigar a jihar da ke fama da rikici.

Kwanan nan yan bindigan sun kona gidan kakakin majalisar dokokin jihar, Nasiru Magarya, a garin Magarya dake karamar hukumar Zurmi.

Mazauna garin da suka tsere sun shaidawa manema labarai cewa akalla mutane bakwai aka kashe a karamar hukumar Shinkafi cikin kwanaki bakwai da suka gabata.

Daga cikin mamatan akwai tsohon kamsila na mazabar Jangeru da ke Shinkafi, Abubakar Mai-Sallah, wanda aka kashe a makon da ya gabata a gidansa da ke garin Jangeru.

Mazauna garin sun ce yayin da farmakin da sojoji ke kaiwa ‘yan bindigar ke iya samun nasara a wasu yankuna, ba a ji tasirinsa ba a kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: