Dalilan da yasa na koma jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode

0 114

Tsohon ministan surufin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya koma jam’iyyar APC da ke mulki.

An gabatar da Fani-Kayode a gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja karkashin jagorancin shugaban riko na jam’iyyar kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a yau Alhamis.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle na daga cikin wadanda suka karbi Fani-Kayode a jam’iyyar APC a fadar gwamnatin.

A yayin da yake magana, Fani-Kayode ya ce ya taimaka matuka wajen sauya shekar gwamnonin jam’iyyar PDP uku zuwa APC.

Tsohon kakakin tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, wanda ya ce yana daga cikin wadanda suka kafa APC, ya kara da cewa ya koma APC ne domin hadin kan kasarnan.

Ya shawarci ‘yan Najeriya da kar su yarda wani mutum ko wata kungiya ta raba su ko su sa kasar ta wargaje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: