‘Yan bindiga sun kai hari garin Maganar Jibiya a yankin karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina, inda suka kashe DPO na ‘yansanda, DSP A. A. Rano tare da wani soja.

An rawaito cewa DPOn ya jagoranci wata tawaga domin tarwatsa ‘yan fashin dajin lokacin da suka yi masa kwantan bauna suka kashe shi tare da sojan.

Wani mazaunin garin mai suna Muhammad Aminu, yace ‘yan bindigar sun kuma raunata wani babban jami’an soja da aka ce sunansa Kanal Masoyi tare da sace wasu mutane da ba a san yawansu ba a harin.

Mamacin DPOn tare da wasu sojoji ya samu nasarar korar ‘yan fashin dajin da suka kawo hari kauyen Daddara dake karamar hukumar ta Jibia, inda aka kashe dagaci da wasu mutane biyar.

Kakakin yansanda na jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya wallafa hoton mamacin a shafukan sada zumunta daban-daban yana jimamin mutuwarsa, har yanzu bai tabbatar da mutuwar tasa ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: