Gwamnatin Tarayya za ta kaddamar da bincike domin bankado yadda aka shigo da gurbataccen man fetur dauke da sinadarin methanol sama da kima..

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a yau yayin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako mako wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan, wanda ya ce gwamnati na taka-tsan-tsan wajen tunkarar al’amuran da suka shafi gurbataccen man fetur, ya nemi a kara hakuri domin kawo karshen binciken kafin duk wani yunkuri na bankado masu hannu a cikin lamarin.

Ya kuma ce za a yi la’akari da al’amuran da suka shafi ababan hawa da suka lalace sakamakon lamarin da ba a saba gani ba wajen tunkarar lamarin.

Timipre Sylva ya ce Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), zai iya magance halin da ake ciki a yanzu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: