Yan bindiga sun kai hari wani kauye a karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto

0 122

Yan bindiga sun kai hari wani kauye a karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto, inda suka kashe mutane shida, ciki har da matan aure biyu.

An rawaito cewa da sanyin safiyar jiya ‘yan bindigan suka mamaye kauyen Saminaka, wanda mazaunansa galibi mafarauta ne.

Harin yazo ne bayan yawancin mazauna kauyen sun tafi farauta.

Babu tabbas ko harin yana da nasaba da kisan gungun ‘yan bindiga 13, wadanda suka kai hari garin Tangaza a ranar Asabar.

Wasu fusatattun mutane a ranar Asabar sun kashe tare da kone gawarwakin ‘yan bindiga 13, wadanda suka kai hari suka kashe mutane hudu a garin Tangaza.

Kazalika, ‘yan bindiga sun kashe mutane biyar tare da raunata wasu biyar a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi dake makotaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: