‘Yan fashin daji sun kai hari kan wata rugar Fulani a jihar Kaduna

0 96

‘Yan fashin daji sun kai hari kan wata rugar Fulani a kauyen Barakal-Lahu dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda suka kashe wani mutum mai suna Imam Abubakar.

An rawaito cewa ‘yan fashin dajin sun yi awon gaba da wani adadi na shanu da ba a san yawansu ba.

Hakimin kauyen, Alhaji Muhammad Abdullahi, wanda ya tabbatar da harin ga manema labarai, yace lamarin ya auku da misalin karfe 12 da kwata na dare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: