Yan kato da gora sun doki wani mutum wanda yayi sanadiyyar rayuwar sa a karamar hukumar Kirikasamma

0 172

Yan kato da gora sun doki wani mutum mai suna Adamu Salisu dan shekara 25, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwarsa a garin Madachi na karamar hukumar Kirikasamma ta jihar Jigawa.

Wani mazaunin garin, Bala Madachi, ya shaidawa editan mu cewa ana zargin mamacinne da sace-sace.

Kakakin yansanda, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a Dutse.

Yace lamarin ya auku a ranar Asabar a garin Madachi bayan mamacin ya fito domin diban ruwa a wata tuka-tuka dake kallon gidansa.

Shiisu Adam yace daga cikin wadanda aka kama dangane da kisan akwai Mallam Idi da Usman Mallam da kuma Isa Yahuza, dukkaninsu mazauna garin Madachi a karamar hukumar Kirikasamma.

Yace za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: