Rundunar ‘yan sandan Jihar Enugu ta ce ta gano wata hanyar safarar mutane ta ƙasa da ƙasa da ake zargin tana da alaƙa da karuwanci, inda ta kama wata mata ‘yar shekara 50 mai suna Ibekwe Nkiru tare da ceto wata budurwa ‘yar shekara 20.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Daniel Ndukwe, ya fitar a daren Laraba.
Sanarwar ta ce jami’an ‘yan sanda na sashen Igbo-Eze South ne suka aiwatar da kamen a ranar 16 ga Janairu, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri cikin gaggawa.
Binciken farko ya nuna cewa budurwar, ‘yar asalin Jihar Abia, an yaudare ta ne ta bar aikinta a garin Aba tareda alkawarin samun aiki mafi tsoka a ƙasar Senegal.
Sai dai daga bisani ‘yan sanda suka ce aikin da aka yi mata alkawari ya kasance na karuwanci ne, wanda tarko ne cikin dabarar safarar mutane.
Rundunar ta ce a wannan rana da misalin ƙarfe 7:10 na yamma, wacce ake zargin ta kai budurwar waniwajen tsafi a ƙauyen Alor-Agu da ke Karamar Hukumar Igbo-Eze South, bisa umarnin sauran ‘yan ƙungiyar safarar da ke gudun hijira.
‘Yan sanda sun ce bayan samun bayanin da misalin ƙarfe 8:00 na dare, jami’an suka garzaya wurin inda suka kama wacce ake zargin tare da ceto budurwar, wadda daga bisani aka mayar da ita ga iyalanta, yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin zurfafa bincike domin cafke sauran waɗanda ke da hannu a wannan laifi.