‘Yan Sanda Sun Kama Mutum Mai Shekaru 35, kan zargin lalata da yarinya ‘yar shekaru 16 a Yobe

0 242

Rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 35 a duniya,  bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 16 a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a ranar Litinin, ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan samun rahoton gaggawa daga jama’a.

Sanarwar ta bayyana cewa wanda ake zargin, Aliyu Yarima dan Karamar Hukumar Potiskum, ya yaudari yarinyar tare da ba ta abin sha mai haɗe da ƙwayoyi masu sa maye.

‘Yan sanda sun ce abin shan ya sa yarinyar ta suma, lamarin da ya ba wanda ake zargin damar kai ta gidansa inda ake zargin ya yi aika aikar.

Rahoton ya nuna cewa yarinyar ta samu munanan raunuka a jikinta, lamarin da ya jinkirta bayyanar da abin da ya faru.

Daga bisani an garzaya da ita Babban Asibitin Babbangida, inda gwajin likitoci ya tabbatar da cewa an yi mata aika-aikar.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ana cigaba da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken, tare da kira ga jama’a su rika kai rahoton irin wadannan laifuka da wuri.

Leave a Reply