

Yansanda a jihar Jigawa sun kama wani malamin makaranta mai shekara 38 bisa zargin sace dalibarsa da yi mata fyade a yankin karamar hukumar Dutse.
Kakakin rundunar yansandan jiha, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa ga manema labarai.
Wanda ake zargin, wanda malamin makaranta ne a makarantar sakandiren gwamnati ta jeka ka dawo a Wurno, ya dauke dalibarsa daga kauyen Wurno zuwa wani gida a birnin Dutse, inda ya kwana da ita tare da yi mata fyade.
An kai malamin da dalibar zuwa cibiyar da ake kai wadanda aka yiwa fyade a babban asibitin Dutse domin duba lafiyarsu.
Shiisu Adam yace a lokacin da ake bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Yace har yanzu ana cigaba da bincike kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.