‘Yan Sandan Edo Sun Kama Mutane Tara da Ake Zargi da Aikata Laifuka Daban Daban Masu Alaka Da Tsaro

0 270

Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta ce ta kama mutane tara da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane, kungiyoyin asiri, fashi da makami da sauran laifuka masu alaka da tsaro a birnin Benin.

Mai magana da yawun rundunar, Eno Ikoedem, ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, inda ta ce kamen ya biyo bayan ayyukan sintiri da bincike na sirri da aka gudanar cikin makon da ya gabata.

Ta ce rundunar ta samu bayanan sirri kan karar harbe-harbe a wani gida da ke titin Erediuwawa a kusa da Sapele Road, lamarin da ya kai ga cafke wani mutum mai suna Emmanuel Omorodion, tare da kwato bindiga mai bututu biyu da harsashi guda.

A wani samame na daban, ‘yan sanda sun kai farmaki kan wata kungiya da ake zargin tana aikata garkuwa da mutane da ayyukan kungiyoyin asiri a yankin Eyaen, inda aka kama wanda ake zargi jagoransu, Usifo Omojale, da wasu mutum biyar.

Rundunar ta ce wadanda aka kama sun amsa kasancewarsu mambobin kungiyar asiri ta Aye, yayin da ake ci gaba da bincike domin tarwatsa dukkanin hanyar sadarwar da ke da alaka da laifukan.

Haka kuma, a wani aiki na daban, ‘yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami a Unguwar Uwadia, inda aka kwato adda uku, kwamfuta, wayar iPhone da wasu kayayyaki.


Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta jaddada kudurinta na ci gaba da sintiri da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, tare da kira ga al’umma da su rika bayar da sahihan bayanai domin kare rayuka da dukiyoyi.

Leave a Reply