Yobe Tabi Layi Zata Tura Ɗalibai Ƙatare Domin Karatu

0 207

Gwamnatin jihar Yobe tace zata dauki nauyin dalibai 228, su samu digiri a bangaran karatun aikin likita wato Medicine da Paramedics da kuma Engineering a shekara mai zuwa.

Gwamnan jihar Mai Mala Buni shine ya bayyana hakan a jiya a garin Damaturu yayin karbar rahoton kwamatin jihar na tallafin karatun dalibai na kasar waje.

Gwanan wanda ya samu wakilcin Alhaji Baba Malam-Wali sakataran ayyukan Gwamnatin Jihar, ya bayyana cewa bada tallafi ga dalibai zai kara musu karfin gwuiwar yin karatu ta yanda za’a rage yawan masu zaman banza.Ya ce, za’a kara kaimi na musamman akan ilimin mata da kuma mutane marasa karfi, sannan ya kara da cewa bangaran ilimi shine wanda za’a bawa fifiko a Gwamnatin sa.

Dr Sheriff Almuhajir shugaban Kwamatin bada tallafin dalibai na kasashen waje, yace kwamatin zatayi kokarin yin adalci akan aikin da aka bata, ba tare da nuna banbanci a tsakanin wadanda zasu amfana da shirin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: