Ku Cigaba Da Karɓar Yagaggun Kuɗi – CBN

0 220

Babban bankin kasa CBN ya musanta rahotonnin da ke cewa bankuna za su daina karbar kudaden da suka yage daga hannun kwastomominsu daga ranar 2 ga watan Satumba.

Daraktan yada labaran bankin na CBN Mr Isaac Okorafo ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta wayar tarho.

A ‘yan kwanakinnan dai ana ta yada jita-jitar daina karkar duk kudin da ya yage a bankuna inda ya ce, hakan ba gaskiya bane, don kuwa koda wa’adin ya cika bankunan za su cigaba da karbar irin wadannan kudade.

Haka kuma ya ja hankalin mutane da su cigaba da kai yagaggun kudin bankuna domin sanyawa a asusun sub a tare da wata matsala ba.

Isaac Okorafo, ya kara da cewa, bankin na CBN ya bada dama ne daga watan Yuni zuwa Satumba domin ban kunan kasuwanci su tantance irin wadannan kudade wadanda ba za a cigaba da amfani da su ba.

Daraktan yada labaran na CBN ya kuma bukaci al’umma da su kai masa rahoton duk wani banki da suka kaiwa kudin ya ki karba ta lambar waya 07002255226 daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yammacin kowacce rana.

Auwal Hassan Fagge (WBM)

Leave a Reply

%d bloggers like this: