Za a iya kallon masu garkuwa da mutane a matsayin yan ta’adda a cewar Abubakar Malami

0 81

Ministan Shari’a na Kasa kuma Babban Lauyan Gwamnati Abubakar Malami SAN, ya bayyana cewa daga yanzu za’a iya kallon masu Garkuwa da mutane a matsayin yan ta’adda.

A makon da ya gabata ne wata babbar Kotu wanda take zamanta a Abuja ta bayyana yan bindiga da masu Garkuwa da mutane a matsayin yan ta’adda.

Daraktan Shigar da Kara na Ma’aikatan Shari’a ta Kasa Barista Muhammed Abubakar, shine ya shigar da karar a madadin gwamnati.

Da yake jawabi a jiya, lokacin da ya bayyana a gidan Talabijin na Channels Tv, Abubakar Malami, ya ce duk wanda suke amfani da makami ko kuma karfi wajen sace mutane daga yanzu sun zama yan ta’adda.

Ministan ya ce gwamnati ta samu izinin Kotu kan ayyana yan bindigar a matsayin yan ta’adda, saboda haka zata buga hakan a Jaridu.

Kazalika, Ministan ya ce bashi da masaniya kan saka sunan Gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano, a matsayin mutanen da Hukumar EFCC take sanyawa ido.

Leave a Reply

%d bloggers like this: