Ana cigaba da lalumo fiye da mutane 50 da suka nitse a jirgin ruwa a jihar Kano

0 100

Adadin mutanen da suka mutu a sanadiyar Kifewar Jirgin Ruwa a Jihar Kano sun kai 29 zuwa yanzu.

A ranar da lamarin ya faru, gawarwakin mutane 20 ne aka tsinto a ciki ruwa ciki harda Kananan yara yan Firamare.

A Lokacin da Manema Labarai suka ziyarci wurin da lamarin ya faru Kakakin hukumar Kashe Gobata ta Jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da gano gawarwakin 9 a lokacin.

Jirgin ya kife ne a lokacin da Fasinjojin Jirgin wanda Daliban Makarantar Madinatu Islamiyya School suka baro garin Badau zuwa Bagwai, domin halartar Mauludi fiyayyen halitta.

Kawo yanzu duk gawarwakin mutanen da aka fito dasu daga cikin Kogin an binne su kamar yadda Addinin musulunci ya tanada.

Manema Labarai sun rawaito cewa daga cikin mutanen da lamarin ya shafa sun hada da Mata 8 wanda suka kawo ziyara garin daga Unguwar Naibawa ta birnin Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: