Gwamnatin jihar Jigawa ta kasance ta daya a arewacin Nigeria kuma ta biyu a Najeriya wajen samar da ruwan sha ga alumma

0 91

Gwamnatin jihar Jigawa ta kasance ta daya a arewacin Nigeria yayinda ta kasance ta biyu a Nigeria wajen samarda ruwansha ga alumma.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar shine ya sanar da hakan a jiya lokacin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa kan yadda za a magance matsalar karancin ruwan sha a yankin Sahara Na Afirka.

Gwamnan ya ce taron wanda sashen samarda hadin kan kwararru a Afirka da ma’aikatar alamurran kasashen waje suka shirya zai taimaka wajen kara inganta hanyoyin samarda ruwansha da kuma samarda Nagartattun tsare-tsaren da za a yi amfani dasu a gaba wajen samarda ruwansha.

Alhaji Muhammad Badaru yace gwamnati tana bada kulawa ta musamman ga bangaren samarda ruwansha ta hanyar bullo da sabbin manufofi da dabaru wanda hakan ya sanya jihar ta yi fice wajen samarda ruwansha a arewa da kuma kasa baki daya.

A nasa jawabin babban daraktan sashen samarda hadin kan kwararru a Afirka Ambassada Rabiu Dagari yace an tsara taron tattaunawar ne da kwararru ta yadda za a samu sabbin hanyoyi na kula da kuma magance matsalar karancin ruwansha a yankin sahara na afirka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: