Za a samu karancin gurasa saboda tashin farashin fulawa

0 145

Akwai yiwuwar nan ba da dadewa ba a samun karancin gurasa kasancewar masu sarrafa ta suna barazanar dena sarrafawa saboda tashin farashin fulawa.

Shugabar kungiyar masu sarrafa gurasa a jihar Kano. Hajiya Amina Abdullahi, tace farashin fulawa yana tashin gwauron zabi a kowace rana kuma suna shan wahala wajen cigaba da kasuwancin.

Amina Abubakar ta kara da cewa tunda farko ‘ya’yan kungiyar sun dauki tsauraran matakan cigaba da kasuwancin da suka hada da rage girman gurasa amma hakan bai samar da sakamakon da ake bukata ba.

Tace baya ga sayen fulawar da tsada sosai, suna kuma fama da rashin ingancin fulawar.

Sakataren kungiyar, Ahmad Rufa’i Tanko, yace lamarin ya jefa wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar a bashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: