Umahi ya ce a wata mai zuwa Shugaba Tinubu zai kaddamar da aikin titin mai tsawo kilomita 1,000 a Jihar Kebbi. Da yake tattaunawa a Jihar Kebbi da masu ruwa da tsaki kan rukunin farko da na biyu na aikin jihohin Kebbi da Sakkwato, Umahi ya shaida musu cewa aikin zai fara ne daga bangaren da ke da nisa kilomita 258 a jihar.