Za’a yiwa mutane 1,000 tiyatar Yanar Idanu kyauta a Jihar Jigawa

0 186

Maaikatar lafiya ta jihar Jigawa ta amince da yiwa mutane dubu daya aikin tiyatar Yanar Idanu kyauta da gidauniyar Darrul Imara  Charity foundation da hadin gwiwar gidauniyar Hilal foundation dake kasar Turkiyya suka dauki nauyi.

Tawagar ta gidauniyar Hilal zata iso birnin jiha Dutse a ranar Talata domin fara aikin tiyatar Yanar Idanu da za a fara daga ranar Laraba mai zuwa shida ga wata zuwa 11 ga wata.

A sanarwar da jamiin kula da harkokin Idanu na maaikatar AU Abdulrahman ya sanyawa hannu ta ce za a gudanar da aikin tiyatar Yanar Idanun ne kyauta a Asibitin Sambo dake Dutse da kuma asibitin Idanu na Huda Eye Clinic.

Dangane da haka ne, maaikatar lafiya ta jihar Jigawa ta bada umarnin tantance masu matsalar idanu 40- 40 daga kowacce karamar hukuma daga yau Litinin domin yi musu aikin.

Sanarwar ta kara da cewar kananan hukumomi ne zasu bada motoci domin dauko wadanda aka tantance zuwa Dutse domin yi musu aikin Haka kuma tuni aka aikewa da kananan hukumomi jaddawalin ranekun aikin tiyatar Yanar Idanu na kowacce karamar hukuma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: