Diyar shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Zahra Buhari-Indimi ta baiwa jaridar SaharaReporters kwanaki bakwai ta janye labarin da ta wallafa kan harkallar handame naira biliyan 51 da aka saka sunan ta a ciki.

Zara ta ce babu gaskiya a wannan labari.

Ta bayar da wa’adin ne a wata wasika da ta aika wa jaridar ta hannun lauyanta, Nasiru Adamu, wani Babban Lauyan Najeriya (SAN).

A cikin wasikar, Zahra Indimi ta kuma nemi jaridar ta wallafa neman gafararta kowa ya gani a jaridun kasarnan nan da kwanaki bakwai.

Sahara Reporters ta ruwaito cewa Nasiru Danu, wani na hannun daman Shugaba Buhari da wasu manyan jami’an hukumar kwastam ta Najeriya, a kwanannan ya damfari gwamnatin Najeriya naira biliyan 51.

Jaridar ta kuma kara da cewa naira biliyan 51 din da Danu ya waske da su, na kudaden shiga ne na “Hukumar Kawastan”

Rahoton ya bayyana cewa an dankara wa gidauniyar Zahra-Indimi naira biliyan 2.5 wanda shi ma Danu din daya ne daga cikin masu mallakin gidauniyar.

Zahra ta karyata wannan labari sannan ta baiwa jaridar Sahara Reporters wa’adin kwanaki bakwai su janye wannan labari, sannan su bata hakurin da za su wallafa a manyan jaridun kasar nan, ko kuma a hadu a kotu.

Ta ce lallai a cire wannan labari a shafin jaridar, da kuma shafukan sada zumunta na Tiwita da Facebook.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: