Kimanin masu hakar ma’adinai 100 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a rana guda a yankin Kananan Hukumomin Maru da Aka a Jihar Zamfara.

Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, ya bayyana cewar ’yan bindigar sun kuma kashe mutum 10 tare da mamaye wani wurin hakar ma’adanai a yankin.

Sarkin Anka ya sanar da haka ne yayin tattaunawa da Mayan Hafsoahin Tsaro da suka ziyarci Jihar a Gusau don ganawa da Gwamna Matawalle kwamnadojin soji kan kawo karshen mastalar ’yan bindiga da ke ci wa jihar tuwo a kwarya.

Basaraken wanda ya ce ’yan bindiga ba sa ga-maciji da masu hakar ma’adinai a jihar, ya bayyana cewa labarin harin na ranar 2 ga Maris bai bazu sosai ba ne saboda a lokacin hankula sun karkata ne zuwa ga batun garkuwa da Dalinayn Makarantar Jangebe.

“’Yan bindiga sun addabi masu aikin hakar ma’adanai tare da kwashe kudadensu da dukiyoyinsu.

“Akwai rashin jituwa tsakanin masu hakar ma’adanai da ’yan bindiga a jihar.”

Sarkin ya yi mamakin dokar hana tashin jirgi da Gwamnatin Tarayya ta sanya a Jihar bisa zargin hadin bakin masu hakar ma’adinai da ’yan bindiga wajen fasakwaurin makamai da kuma musyarsu da zinaren da aka bako.

“Mun yi mamakin sanarwar ‘hana shawagin jirgi’ da aka sa wa jiharmu kan zargin fasakwaurin makamai da kuma hakar ma’adanai ba bisa ka’ida, alhali ko filin jirgi babu a jihar.

“Mun san akwai jihohin da suke da matsalar tsaro fiye da Zamfara kuma muna sa ran cewa idan za a bayar da irin wannan umarnin, ya kamata su ma ya hada da su.

“Mutanenmu masu aikin hannu da aka ba kananan lasisin hakar ma’adinai, sun taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin jihar kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar ’yan gudun hijira a jihar ta hanyar tallafa musu,” inji shi.

Ya kuma yi kira da a kara yawan jami’an tsaro don yakar ’yan ta’adda a jihar.

“Shirin samar da zaman lafiya da tattaunawar da gwamnanmu ya yi ya zama dole saboda a yanzu muna da kasa da jami’an tsaro 5,000 ne da ke yaki da ’yan bindiga l 30,000.”

Sarki Attahiru Ahmad ya tabbatar wa shugabannin tsaron cewa mutanen jihar za su ci gaba da yi musu addu’ar samun nasara.

Sannan ya kuma bukaci Babban Hassan Tsaro, Lucky Irabor da ya tabbatar da hadin kai a tsakanin dukkan bangarorin sojoji yayin gudanar da ayyukansu domin toshe duk wata kafa ga masu aikata laifi.

Da yake amsawa, Shugaban Hafsoshin tsaron ta yaba da rawar da sarakunan suka taka wajen yaki da aikata laifuka sannan ta bukace su da su ci gaba da jan hankalin mabiyansu wajen ba da sahihan bayanai da za su kai ga kame ’yan ta’adda.

A nasa jawabin, Gwamna  Matawalle ya ba da tabbacin gwamnatinsa na karfafa zaman lafiya da tattaunawa tare da tallafa wa hukumomin tsaro wajen ci gaba da kai hare-hare kan ’yan bindiga da ba su tuba ba.

Asalin labarin@

https://aminiya.dailytrust.com/yadda-yan-bindiga-suka-yi-garkuwa-da-masu-hakar-maadinai-100-a-zamfara

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: