Yanzu -Yanzu : An yiwa Gwamna Badaru allurar rigakafin korona

0 78

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru ya yi allurar rigakafin Korona a gidan gwamnatin jihar dake Dutse.

Allurar wadda daya daga cikin likitocin gidan gwamnatin ya tsirawa gwamnan allurar da misalin karfe 1: 45 na yau Laraba.

Gwaman ya kuma karbi shaidar yi masa allurar mintuna kadan da yi masa allurar.

Daga bisani Gwamnan ya shaidawa yan Jaridu cewa allurar rigakafin korona bata da illa saboda ta samu shaidar hukumar lafiya ta duniya.

Yace mataimakin sa Muhammad Namadi da wasu daga cikin kwamishoni suma anyi masu rigakafin ta korona.

Ya kuma cewa malaman addinai da ma’aikan lafiya a Jihar suna daya daga cikin wadanda za’a fara yayiwa allurar rigakafin.

Bayan haka Badaru ya hori ‘Yan Jigawa su amince ayi musu rigakafin, yana mai cewa sunna ahankali, allurar rigakafin zata iso lungu da sako na Jigawa.

Jihar Jigawa ta sami addadin allurar rigakafin korona 68,520 daga gwamnatin tarayya wanda yayi daidai da kashe daya na cikin yawan al’umma mai yawan mutum kimanin miliyan biyar.

A jihar Kano Kuma gwamnatin Abdullahi Ganduje ta bayyana wasu asibitoci har 509 da za a rika yi wa mutane rigakafin Korona.

Sai dai kuma yan Najeriya da dama na cigaba da bayyana ra’yoyin su game da rigakafin Korona din.

Wasu har yanzu sun kafe cewa ba za su yi rigakafin ba domin ba su amince da cutar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: