Labarai

‘Zanyi aiki tukuru tare da masu sarautun gargajiya wajen ciyar da jihar Jigawa gaba matukar an zabe ni gwamnan jihar a shekarar 2023’ – Mustapha Lamido

Mai Martaba Sarkin Kazaure Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, ya karbi Bakuncin Dan Takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin tutar Jam’iyar PDP Alhaji Mustapha Sule Lamido, wanda ake kira Santuraki a fadarsa.

Ziyarar tamkar wasu hanyoyin tuntuba da neman Albarkar masu sarautar gargajiya da masu ruwa da tsakin Jihar Jigawa ne.

An bada rahotan cewa ziyarar ta samu karbuwa da kuma tagomashi daga wuraren masu sarautun gargajiya.

Da yake Jawabi, Mustapha Sule Lamido, ya bawa Sarkin tabbacin cewa Jam’iyar PDP zata gudanar da gangamin yakin neman zaben ta, cikin Ladabi, da mutumta Jama’a.

A cewar Mustapha Sule Lamido, zaiyi aiki tare da masu Sarautun Gargajiya wajen ciyar da Jihar Jigawa gaba, matukar an zabe shi Gwamnan Jiha a shekarar 2023.

Da yake mayar da Jawabi, Mai Martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu, ya bukaci mutane su kasance masu Jin tsoron Allah, da kuma kiyayewa da Dokokin sa, tare da daukar kansu a matsayin yan uwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: