A ranar Talata ne kwamitin Ilimi na Majalisar Dattijai ya ce zai bukaci yin garanbawul a dokar da ta kafa Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta yadda za a hana ’yan kasa da shekara 16 samun guraben karatu a fadin jami’o’in cikin gida Najeriya.

A cewar kwamitin, bai kamata abar dalibai masu kasa da wadannan shekarun su sami guraben karatu a jami’o’i ba, duba da kuruciyarsu wajen gane muhimman abubuwan da za a koya musu.

Mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Akon Eyakenyi ya bayyana hakan yayin ziyarar gani da ido da yayi zuwa shalkwatar JAMB din, ya ce sun gano wasu muhimman wurare da kuma manyan bangarori guda biyu da suke bukatar kwaskwarima a hukumar domin a inganta ta.

Sanata Akon ya jaddada muhimmancin ilimin zamani ga makomar kasa Najeriya ya ce bangaren na bukatar cikakkiyar kulawa da sa ido domin a farfado da kuma inganta shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: